Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Shugaban kungiyar a wannan karo ne kana shugaban kasar Ghana, Nana Afuko Addo, ya kira taron wanda zai gudana ta kafar bidiyo.
Batun ci gaba da amincewa da kasar Guinea mamba a kungiyar bayan da sojoji suka kifar da mulki na daga cikin batutuwan da taron zai tattaunawa akansu.
Tun dai bayan aukuwar lamarin kasashen yankin musamman makobtan kasar ta Guinea, sun yi gum da bakunansu.
Najeriya dai a nata bangare ta yi tir da juyin mulkin, yayin da shi kuwa shugaban Ivory Coast, Allasan Ouatara, ya kasance na farko da ya tattauana da Kanal Mamady Dounbiya, wanda ya jagoranci juyin mulkin inda ya bukaci da sallami tsahon shugaban kasar Alpha Conde da sojoji ka rike da.
342/